14 Mayu 2025 - 11:49
Source: ABNA24
Jawabin Shekh Zakzaky H A Rufe Mu’utamar Aaam Na Ittihadush Shu'ara'i

Ranar Talata 15 ga watan Zulqa’ada 1446 (13/5/2025) Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin rufe Mu’utamar da Mawakan Ittihadush Shu’ara’I Harkatil Islamiyyah suka shirya a Abuja.

A yayin jawabinsa ga dimbin mawakan da suka hadu a gidansa a yammacin Talatar, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara da taya su murnar zagayowar watan Zulqa’ada, wanda aka haifi Imam Ridha (AS) da ‘yar uwarsa Sayyida Ma’asuma (SA) a cikinsa. Yace: “Taronku ya zo daidai da lokacin Mauludin Imam Ridha (SA), wanda a shekarun baya mun saba mukan dauki kwanaki ne muna yi”.

Ya yi bayani dangane da ilimin Imam Ridha (AS), da irin yadda ya rika warware shubuhohi da amsa tambayoyin mulhidai da masu taqamar sani a lokacinsa. “Za mu iya cewa duk wani abu wanda zai zo nan gaba, lallai zai zama akwai mu da makami na maganinshi wanda ya gabata daga wajen A’imma (AS). Kuma muna samun irshadi na Sahibul Asr waz Zaman (AS) a duk lokacin da muke harkokinmu”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana muhimmancin waka da mawaka a tarihin Musulunci, inda ya jaddada cewa, waka tana daga makamin da ake amfani da ita don isar da sako. “Manzon Allah (S) ya yi amfani da wannan makamin, ya kuma amfana da shi ta wajen yada sako”.

Da yake bayani dangane da kida, Jagora (H) ya bayyana rashin aibinsa idan bai kasance na lagawu ko lahawu ba. “Akwai kida wanda yake ‘aala’ ne na lagawu, to lagawu ne haramun. Abinda ake ce ma lagawu shi ne yasasshen magana, kamar ace ana batsa, ko wani kida, kamar yadda Imam Khomaini a Tahrirul Wasila yace, ko wani kida da ya danganci ma’abota lahawu (wargi). Kamar akwai kidan da ake yi ace masa wannan kidan na ‘yan bori ne, misali. Ko kuwa wannan kidan karuwai ne. Ko wannan kidan ‘yan daudu ne. To in wannan ya kebanta da ma’abota lahawu (wargi), to tunda lahawun haramun ne, shi ma kidansa zai zama haramun.

“Saboda haka, nau’in kade-kade in dai Lahawu da Lagawu suka shigo ciki, to su ne haramun. In aka yi amfani da ‘aalan’ lagawu da lahawu, to sai ya koma haramun. Amma idan bai kai ga haka nan ba, to yana iya zama ba laifi da shi”.

Ya kawo misalin yadda mutanenmu suke da kade-kade iri-iri a da, kamar kidan noma, wanda in ana yi manomi kan kara kaimi wajen aikinsa. Yace “Kidan noma kenan, ba laifi da shi. Akwai kuma kidan mayaka a lokacin yaki, shi ma akan yi shi. Akwai kuma kidan masu sana’o’i iri-iri, magina ne, makera ne, duk suna da kade-kadensu”.

Jagora (H) Yace: “Abubuwan da ake musu kidan, in basu haramta ba, to sai ya zama kidan ma bai haramta ba. In abinda ake ma wakan ya haramta, to irin kidansa, in dai nasa ne ya kebanta da shi, sai ya zama shi ma haramun ne. Saboda haka, ba za a dauko kida irin na lahawu a saka shi a abin kirki ba”.

Da yake magana dangane da wakar mata, Jagora (H) ya bayyana cewa ko a da can akwai mawaka mata, amma suna karanta waken ne ba suna karya murya su raira ba. Don haka ya bayyana cewa: “Idan wake ne wanda (mata) za su raira, to idan duk cikansu muryoyi ne (na mata da yawa suka hadu waje guda) ba muryar mace daya ba, to ba laifi da shi. Saboda haka in za su yi waken ba laifi su yi gabadaya, ko kuma in ana wake su yi amshi (cikin jam’insu)”.

A nan ne kuma Shaikh Zakzaky (H) ya ja hankalin sauran mawakan Musulmi akan rashin dacewar yin waka tare da rawa da ‘yan mata. Ya ba da misali da cewa: “Akwai wani Babangida Mafaka da ‘yan mata suna wake. ‘Jayyid’, amma ba kyau su yi rawa. Wake dai za su iya yi da murya daya, amma rawa ba kyau. Bai kamata mace ta rika tika rawa ba, wai tana yabo ba. Rawan bai dace ba, amma dai wake yana da kyau in suka (hadu suka) yi da murya guda”.

Jagora ya kawo yadda ake kokarin kange al’umma daga fahimta da komawa zuwa ga Ahlulbaiti (AS), inda ya yi kira ga al’umma akan riko da wasiccin Manzon Allah (S) na riko da Alkur’ani da Iyalan gidansa (AS). Yace kuma: “Ba mujarradin kace kana son Iyalan Annabi ba ne, akwai bukatar ka san su, ka san ilimin da suka koyar, ka kuma dabi’antu da ilimin da suka koyar, ka shiriya da shiriyarsu”.

Shaikh Zakzaky ya nanata cewa: “Wannan kuwa ba zai yiwu ba, sai ka san su (Ahlulbaiti din), ka san abinda suka koyar. Kuma abinda suka koyar ne ake kokarin kar a sani, don haka aka dabaibaye mu da sunannakin da ake kyamamawa, ace Shi’a-Shi’a-Shi’a, sai aka maishe shi kamar wani mummunan abu ne, alhali kuma kalmar ma ba mummunan abu ba ne, yana nufin magoya bayan Alhlulbaiti (AS)”.

Ya bayyana yadda kyamatar kalmar Shi’a ya fara kawuwa daga mutane. “Al’umma sun fara fahimta, wannan ya fara kawuwa. Son iyalan Annabi yana tare da musamman Mutasawwufa. Duk Mutasawwufa suna son Ahlulbaiti (AS), kuma kowannensu yana tinkawo da cewa babban waliyin da yake bi daga gidan Annabta ya fito”.

Harwayau, Jagora ya karfafa bukatar masu wake su san abinda suke fada, ta hanyar yin karatu a gaban Malamai, ba kawai sauraron wa’azi ba. Yace: “Kuma lallai ne ya zama kalmomin da ake amfani da su wajen yin yabon nan sun dace da sanin matsayin wadannan mutanen (da ake wakewa). Kar a fadi wasu kalmomin da ake ganin ana yabonsu ne, alhali a wurinsu ya tashi a yabo”.

Ya kuma jaddada muhimmancin yin wakoki wajen isar da sako, inda ya bayyana cewa: “Na san ‘yan uwa da yawa sun ta isar da sako, har ma wani lokaci in suka yi wake, in na tashi sai in ce, ai ma kun gama wa’azi, duk abinda zan fada ma kun gama wake shi”.

Ya kara da cewa: “Na san kuma Allah jikan Shahid Shafi’u Kazaure, duk zaman da muka yi, ko na Imam Ridha ne, ko na Sayyida Zahra, sai ya je ya maishe su wake. Duk abinda aka fada, sai ya koma ya sarrafa shi ya zama wake. To na san nace, yana da kyau daidai wannan lokaci da ake ta hujumi akan wannan al’umma tamu da nau’o’in hujumomi, kun ga yadda aka bullo da batun abinda ake ce ma ‘yan bindiga din nan, da ‘kidnapping’. Na san Malam Uzairu Badamasi ya dan yi dan wake kan ‘kidnapping’ ko?”.

A nan ne Jagora ya yi irshadi ga mawaka akan muhimmancin yin wake-wake akan halin da ake kokarin jefa al’umma a ciki.  “Yana da kyau a yi wake-wake a nuna cewa, wadannan ta’addanci da ake yi, makiyanmu ne suka kitsa, suka kawo mana. Mu ba ‘yan ta’adda ba ne, ba wata kabila kuma da za a jingina mata ta’addanci”.

Ya kara da cewa: “Yana da kyau kar a jefa mu a cikin fadan rudani na kabila. Idan mutum ya yi laifi, shi ya yi laifi, ba a jingina ma mutanen garinsu, ko mutanen kauyensu, ko mutanen kabilarsu”.

Yace: “Yana da kyau fadakarwa (akan manufar makiya akanmu) ya zama ya shiga wake. A rika fadakar da mutane, su yi hattara, kada su fada tarkon makiya wajen jefa mu a fadan kashe-kashe. Wadannan kashe-kashen mu gane, ba wasu ne (ke haddasa shi ba) illa makiyanmu na waje”.

Da yake tsokaci dangane da tsare Shaikh Abduljabbar da mahukunta ke cigaba da yi har yanzu, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa: “Ba mu san wane ‘interest’ su mahukuntan yanzu suke da shi na rike shi har yanzu ba, don ba wani dalili na rike shi. Ganin cewa ‘case’ ne wanda babu yadda za a yi a mizanin hankali a tabbatar da shi.

“Wato mutum ne yake cewa, wannan hadisi an mai da Manzon Allah tamkar kaza kenan. Sai aka ce shi ya ce ma Manzon Allah kaza. Wai to ina kai ka samu wannan? Don yace, wannan ai kamar an raina Annabi (S) ne, an maishe shi tamkar kaza… To sai aka ce, atafau wai shi ya dai wannan kalmar”.

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa, ko mutum ya yarda ko kar ya yarda, mahukunta na baya, sarakai, sun yi wasa da hadisin Annabi (S), sun sa an musu hadisai, kuma sun sa an jirkita musu hadisai, sun yi amfani da su don biyan bukatan kansu”.

Yace, mutane suna ganin kamar tonowa da ake ace wannan Hadisin ba daidai ba ne, kamar zai rusa musu addininsu ne. “Amma kuma lallai addinin nan ba zai tsaya ba, sai an tono wadannan abubuwan da suke ba daidai ba, an ce ba daidai ba ne, don a kare martaban Annabi (S)”.

Bayan da ya kawo misalsalai masu yawa na yadda aka rika jirkitawa tare da kirkiran hadisan karya a baya, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Irin wannan ne ya janyo wasu mutane suka ce, kai ba ruwansu ma da Hadisan gabadaya tunda abin haka ne, suka koma Alkur’anawa”. Yace: “To wallahi gara Bakur’ane sau dubu, da wanda zai karanta Hadisi yace iyayen Annabi (S) na wuta”.

A karshe Jagora ya yi fatan a cigaba da shirya irin wadannan mu’utamarori, da kuma addu’ar Allah ya haskaka al’ummar nan da hasken iyalan gidan Annabi (S), da gyaruwan al’amura har ya zama al’umma ta koma tafarkin addinin Musulunci.

Mu’utamar din, wanda aka faro shi ranar Lahadi da daddare, an shafe kwanaki biyu ana gudanarwa, inda makawan Harka Islamiyyah daga sassa daban-daban na kasar nan suka halarta, tare da wasu daga mawakan addinin Musulunci daga bangarori daban-daban, kamar Alh. Bashir Dandago daga Kano, da Muhammad Zanawi daga Yola.

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

15/Zulqa'ada/1446

13/05/2025

Your Comment

You are replying to: .
captcha